Sunaye: Buhari ya nada manyan darektocin hukumar NSIA

Sunaye: Buhari ya nada manyan darektocin hukumar NSIA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Stella Ojekwe-Onyejeli da Aminu Umar Sadiq a matsayin manyan darektoci ma su kula da hukumar saka hannun jari ta Najeriya (NSIA).

Titilope Olubiyi, kakakin hukumar NSIA, ne ya sanar da hakan a yau, Larabara, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Olubiyi ya bayyana cewar wannan shine karo na biyu da aka nada Ojekwe-Onyejeli a matsayin darekta a hukumar yayin da Umar Sadiq, wanda mataimakin darekta ne a hukumar, aka nada shi a karo na farko.

Ya kara da cewa, sabbin nade-naden zasu kara karfafa aikin hukumar, musamman a bangaren bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Sunaye: Buhari ya nada manyan darektocin hukumar NSIA
Buhari
Asali: UGC

Kazalika, ya ce sabbin nade-naden sun yi daidai da yunkurin hukumar NSIA na bunkasa saka hannun jari a aiyukan da zasu gina Najeriya.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 55, sun kubutar da mutane 760 a Zamfara

Daga cikin bangarorin da hukumar ta NSIA ke kula da saka hannun jari a cikin su akwai: hanyoyi, noma, lafiya, lantarki da ilimi.

A jiya, Talata, ne shugaba Buhari ya dawo Abuja bayan shafe kwanaki hudu a Daura domin kada kuri'a a zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokokin jihohi da aka yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel