Radadin faduwa zabe: 'Yan jam'iyyar AP 10,000 sun sauya sheka zuwa APC

Radadin faduwa zabe: 'Yan jam'iyyar AP 10,000 sun sauya sheka zuwa APC

A kalla 'ya'yan jam'iyyar Accord Party (AP) 10,000 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a garin Ibeju da ke Lekki na jihar Legas.

Tsohon jigo a Accord Party, Injiniya Abiola Okanlawon Olowu ne ya jagoranci masu sauya shekan da aka ce dama tsaffin 'yan jam'iyyar APC ne da suka fice daga jam'iyyar saboda wani rashin jituwa da ya faru a baya.

Oluwu ya ce sun komo jam'iyyar APC ne saboda sunyi imani da jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuma suna son kawa cigaba da yankin Ibeju Lekki na jihar Legas.

DUBA WANNAN: APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

'Yan jam'iyyar Accord Party 10,000 sun koma APC a Legas
'Yan jam'iyyar Accord Party 10,000 sun koma APC a Legas
Asali: Twitter

"Ban taba tsamanin zan zauna tare da Asiwaju balantana har mu tattauna. Asiwaju ya min tambaya inda ya ce: Olowu, za ka dawo jam'iyyar APC ni kuma na amsa da cewa Eh, wannan shine dalilin da yasa ni da magoya baya na muka dawo APC," inji Olowu.

Shugaban karamar hukumar Ibeju-Lekki, Dakta Kemi Surakat ya yi maraba da masu sauya shekar daga Accord Party.

Ya ce ya fi alheri dukkansu su hadu wuri guda domin cimma buri guda a maimakon su ware kowa ya rika gudanar da abinda ya ke so shi kadai.

"Ina mika godiya ta ga Engr. Abiola Olowu, Hon. Akeem Adekoya, Hon. Korede Ojomu da dukkan tsaffin shugabanin Accord Party na karamar hukumar Ibeju-Lekki da kungiyar cigaban Lekki (LCDA) wadanda suka fifita cigaban garuruwansu a kan son zuciya," inji De Kemi Surakat.

Kazalika, Shugaban LCDA, Barrister Mukandasi O.Ogidan ya jinjinawa wadanda suka sauya shekan saboda sun dawo gida, ya kuma yabawa shugabanin APC da suka amince da hakan.

Wadanda suka hallarci taron sauya shekan sun hada da Hon. T.O Shoniyi, Hon. Ogunlaja, Alhaji Tajudeen Oniwonlu, Alhaji Aje-Awa, Hon. Idowu Eletu, Mr Segun Bankole, Chief Tansiru da Hon. Ismail Badmus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel