Kotu ta fadawa Magu ya guji taba Fani-Kayode ba tare da bin doka ba

Kotu ta fadawa Magu ya guji taba Fani-Kayode ba tare da bin doka ba

Alkali mai shari’a John Tsoho na babban kotun tarayya da ke birnin Abuja, ya ja-kunnen hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da su kiyayi kama Mista Femi Fani-Kayode.

John Tsoho, a wani zama da yayi a kotu a makon nan, ya ja-kunnen hukumar EFCC cewa bai dace ta damke tsohon Ministan Najeriya Femi Fani-Kayode da kuma Yinka Odumakin ba tare da ta samu goyon bayan shari’a ba.

Alkali Tsoho yake cewa akwai bukatar ta bi matakan da su ka dace kafin tayi yunkurin cafke tsohon Ministan na PDP da kuma Cif Yinka Odumakin. Hakan na zuwa ne bayan wadanda ake tuhumar sun kai kara zuwa Kotu.

KU KARANTA: Kotu ta bazawa Shugaban NBC wuta da ya hallara gaban ta

Kotu ta fadawa Magu ya guji taba Fani-Kayode ba tare da bin doka ba
Kotu tace ka da a kama Fani-Kayode da Odumakin sai an bi doka
Asali: UGC

Alkalin ya fadawa hukumar ta EFCC cewa damke wadannan mutane ba tare da bin ka’ida ba, zai zama an keta hakkin da dokar kasa ta ba kowane mutum a sashe na 34(a) da kuma 35(1) (4) and (5) na kundin tsarin mulkin kasar.

Femi Fani-Kayode da Takwaran na sa sun shigar da karar EFCC ne su na neman a fitar masu da hakkin su na kama su babu dalili. Alkalin ya ba su gaskiya amma yace babu bukatar hukuma ta fito gaban Duniya ta ba su hakuri.

Tsohon Ministan al’adu da harkar sufurin jirgin saman kasar watau Femi Fani-Kayode yana fuskantar barazana iri-iri na zargin yin gaba da kudin gwamnati a lokacin yana ofis a gwamnatin PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel