Zaben Taraba: An sasauta dokar hana zirga-zirga a Jalingo

Zaben Taraba: An sasauta dokar hana zirga-zirga a Jalingo

Gwamnatin Jihar Taraba da sassauta dokar takaita zirga-zirga na sa'o'i 24 da aka sanya a garin Jalingo babban birnin jihar Taraba a ranar Talata 12 ga watan Maris.

Yanzu an sassauta dokar inda aka baiwa al'umma damar gudanar da harkokinsu daga asubahi zuwa yammacin wato za a iya fara fita daga karfe 4 na asubahi zuwa kare shida na yamma har zuwa wani lokaci nan gaba.

A ranar Talata da ta gabata ne gwamnatin jihar ta sanar ta bakin, babban mai taimakawa gwamnan jihar a fanin watsa labarai, Bala Dan Abu cewa gwamnatin ta saka dokar hana fita na sa'o'i 24 domin tabbatar da doka da oda bayan hukumar zabe INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar.

DUBA WANNAN: Kungiyar Boko Haram ta shiga tsaka mai wuya, kayayakinsu sun kare - MNJTF

An sassauta dokar takaita zirga-zirga a Taraba
An sassauta dokar takaita zirga-zirga a Taraba
Asali: UGC

Sakamakon sassaucin da gwamnatin tayi, ana sa ran al'umma za su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba kuma ma'aikatan gwamnati za su koma bakin aiki.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari ofishin hukumar INEC da ofishin 'yan sanda na jihar Edo inda suka kashe DPO da wasu jami'an 'yan sanda uku.

Har ila yau, 'yan bindigan sun kuma kone wata motar zirga-zirga da suka tarar a harabar ofishin INEC bayan sun lalata kayayakin zabe da dama.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Muhammad Danmallam ya ziyarci inda abin ya faru kuma ya ce za a fara gudanar da bincike nan take domin gano wadanda suka aikata laifin kuma su fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel