NBC: Alkalai sun nemi Ishaq Kawu ya bayyana a gaban Kotu

NBC: Alkalai sun nemi Ishaq Kawu ya bayyana a gaban Kotu

Babban Alkali mai shari’a Folashade Ogunbanjo-Giwa ta bada umarni cewa shugaban hukumar yada labarai na Najeriya (NBC), Ishaq Modibbo Kawu, ya bayyana a gaban kotu a cikin watan gobe mai shiga.

Kotun Tarayya ta yanke wannan mataki ne a makon nan inda aka ce dole Darekta Janar na NBC din watau Modibbo Kawu ya hallara a gaban kuliya a ranar 17 ga watan Afrilun bana inda za a cigaba da shari’a da shi bisa zargin aikata wasu laifi.

A makon nan ne aka nemi Malam Ishaq Modibbo Kawu a shari’ar da hukumar ICPC ta ke yi da shi na cewa ya wawuri wasu kudi har Naira biliyan 2.5 da gwamnatin tarayya ta ware domin kwangilar maida ayyukan hukumar NBC na zamani.

KU KARANTA: Babu maganar tsige Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano

NBC: Alkalai sun nemi Ishaq Kawu ya bayyana a gaban Kotu
Ana zargin Ishaq Modibbo Kawu da satar Naira Biliyan 2.5
Asali: Twitter

Kotu ta bada wannan umarni ne bayan ta gaji da jiran Darektan na NBC ya zo gaban ta. Wannan ya sa a wannan karo Alkali mai shari’a Ogunbanjo-Giwa tace ya zama dole Ishaq Modibbo Kawu ya halarci zaman da za ayi a tsakiyar wata mai zuwa.

Ana dai wannan shari’a ne a babban kotun tarayya da ke cikin Garin Abuja. ICPC mai yaki da cin hanci a Najeriya ta maka Ishaq Kawu ne tare da shugaban kamfanin Pinnacle, Lucky Omoluwa da wani Dipo Onifade, wanda su a kan gan su a Kotu.

Lauya Abdullahi Mustapha, wanda ke kare shugaban hukumar ta NBC ya fadawa kotu cewa rashin lafiya ta hana wanda ake tuhuma iya zuwa kotu. Henry Emore, wanda shi ne Lauyan hukumar ICPC mai kara, ya amince da wannan mataki na kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel