'Yan bindiga sun kai hari caji ofis, sun kashe DPO da 'yan sanda 3 a jihar Edo

'Yan bindiga sun kai hari caji ofis, sun kashe DPO da 'yan sanda 3 a jihar Edo

'Yan bindiga sun kai hari ofishin rundunar 'yan sanda da ke Afuze, hedkwatan karamar hukumar Owan ta Gabas a jihar Edo inda suka kashe DPO tare da wasu jami'an 'yan sandan uku da ke bakin aikinsu.

Kamfanin dillancin Najeriya NAN ta ruwaito cewa 'yan daban sun kuma kai hari ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa INEC a garin na Edo inda suka lalata kayayakin zabe har ma suka kone wata motar sintiri na 'yan sanda da ke harabar ofishin.

Wadanda aka kashe sune Supt. Tosimani Ojo, DPO na ofishin 'yan sandan; Saja Justina Aghomon, wata mace mai dauke da juna biyu, Sufeta Sado Isaac da Kofur Glory David.

DUBA WANNAN: APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

'Yan bindiga sun kashe DPO da wasu 'yan sanda uku a Edo
'Yan bindiga sun kashe DPO da wasu 'yan sanda uku a Edo
Asali: Twitter

Wani shaidan ganin ido, Mr Godwin Ikpekhia ya shaidawa NAN a ranar Laraba cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 8 na daren ranara Talata yayin da galibin jami'an 'yan sandan sun fita ayyukansu a cikin gari.

"Mun ji karar harbin bindiga ne a lokacin babu wanda ya san abinda ke faruwa har sai zuwa safiyar Laraba.

"An kashe DPO tare da wasu jami'an yan sanda uku da ke bakin aikinsu a nan take a cikin caji ofis din.

"Yan bindigan ba su tsaya nan ba, sun wuce ofishin INEC inda suka bude wa 'yan sandan da ke gadin wurin wuta.

"Sun kone kayayakin zabe da kuma wata mota a ofishin na INEC," inji shi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mr Muhammad Danmallam da ya ziyarci inda abin ya faru ya ce za a fara gudanar da bincike a kan lamarin nan take.

Danmallam ya dau alwashin duk wadanda suka aikata wannan laifi za su fuskanci hukuncin da ya dace da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel