‘Yan bindiga 2 sun sace wani Bature da ake aiki a Garin Kano

‘Yan bindiga 2 sun sace wani Bature da ake aiki a Garin Kano

Labari ya zo mana cewa an samu wasu ‘yan bindiga da su ka sace wani Bawan Allah kwanan nan a jihar Kano. Wannan abin takaici ya faru ne a daidai kan titin Dangi da ke cikin Birnin Kano a jiya.

Kamar yadda Jaridar Premium Times ta rahoto, wasu mutane 4 ne da ba a san daga ina su ka fito ba, su ka sace wani kwararren bakanike (watau Injiniya) da ke aiki a Kano. An sace wannan Injiniya ne a jiya da safe.

Wani mutumi da ya bada shaidar abin da ya faru, ya tabbatarwa ‘yan jarida cewa an harbe Direban motar da wannan kwararren bakanike yake ciki kafin a yi gaba da shi da kimanin karfe 7:40 na safiyar jiya Ranar Talata.

‘Yan bindiga 2 sun sace wani Bature da ake aiki a Garin Kano
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Depositphotos

KU KARANTA:Yaron Sule Lamido ya gaza kawo kujerar Sanata a Jigawa

‘Yan Sanda sun dai fitar da jawabi inda su kace babu shakka wannan abu ya faru, kuma tuni aka soma bincike domin gano bakin zaren. Abdullahi Haruna, wanda ke magana a madadin ‘yan sandan Kano ya fadi wannan.

Kuma har yanzu babu wanda ya san ko su wanene mutanen da su ka sace wannan Ma’aikaci da ke kula da kwangilar titi da ake yi a daidai shatale-talen Dangi da ke cikin gari. Mutane 2 ne su ka rufe fuskar su, su kayi wannan aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel