Gwamna Umahi zai koma APC kafin 29 ga watan Mayu – Sanata Ugbuoji

Gwamna Umahi zai koma APC kafin 29 ga watan Mayu – Sanata Ugbuoji

- Dan takaran gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Ebonyi, Sanata Sonni Ogbuoji yayi zargin cewa Gwamna David Umahi zai koma jam’iyyar APC kafin ranar 29 ga watan Mayu

- A ranar Lahadi, 10 ga watan Maris INEC ta kaddamar da Umahi a matsayin wanda ya lashe zabe\

- Umahi ya bayyana zargin a matsayin daya daga cikin farfagandan APC bayan mutanen jihar sn yi watsi da ita

Dan takaran gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Ebonyi a zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris da ya gabata, Sanata Sonni Ogbuoji yayi zargin cewa Gwamna David Umahi zai koma jam’iyyar APC kafin ranar 29 ga watan Mayu ranar rantsar da zababben shugaban kasa da gwamnoni.

Umahi wanda ya sake samun nasara a takara karo na biyu, ya kasance shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar, ya kuma kasance mataimakin gwamnan jihar Ebonyi kafin a zabe shi karo na farko a 2015.

Gwamna Umahi zai koma APC kafin 29 ga watan Mayu – Sanat Ugbuoji
Gwamna Umahi zai koma APC kafin 29 ga watan Mayu – Sanat Ugbuoji
Asali: Depositphotos

Ogbuoji ya bayyana zargin ne a Enugu, a ranar Talata, a taron manema labarai akan sakamakon zaben gwamnoni da na yan majalisan jiha da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu a jihar Ebonyi.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya ba da tallafin firinji ga masu sana’ar kifi a kauyen Yaryasa

Ogbuoji har ila yau ya bada sanarwar zuwa kotu don maida wa Ebonyi yancin ta, ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar da kada su karaya.

Sai dai Gwamna Umahi ya bayyana zargin a matsayin daya daga cikin farfagandan APC bayan mutanen jihar sn yi watsi da ita.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel