Yanzu Yanzu: Saraki ya rantsar da sabon Sanata Alfa daga jihar Kogi

Yanzu Yanzu: Saraki ya rantsar da sabon Sanata Alfa daga jihar Kogi

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Laraba, 13 ga watan Maris ya rantsar da Isaac Alfa a matsayin sanata mai wakiltan Kogi ta gabas a majalisar dokokin kasar.

An rantsar da Alfa a matsayin sanata a gaban sauran tsakwarorinsa a lokacin zaman majalisa.

An tattaro cewa bikin rantsarwar ya biyo bayan kaddamar da Alfa da kotun koli tayi a matsayin ainahin wanda ya lashe zabe a jihar Kogi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairu ta bukaci Sanata Atai Aidoko da ke wakiltan yankin Kogi ta gabas a majalisar dattawa da ya tarkata yanashiyanashi ya bar wa Isaac Alfa kujerarsa a majalisar dokokin kasar.

Kotun ta yanke cewa Alfa ne ya lashe kujerar sanata mai wakiltan Kogi ta gabas a zaben 2015 sannan tayi umurni ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da yayi gaggawan rantsar da shi.

Justis Anwuli Chikere ya soke karar Sanata Aidoko da ke neman a sake duba hukuncin farko da kotu ta zartar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel