Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikata, Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan tarayya, Winifred Oyo-Ita, mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Monguno da ministoci 28 duk sun hallara

- Buhari ya bukaci Amaechi da Adebayo Shittu su bude tarn da addu'a

A yanzu haka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman harda mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. An tattaro cewa an fara taron ne bayan isowar Shugaban kasa zauren majalisar da misalin karfe, 11:09 na safe.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikata, Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan tarayya, Winifred Oyo-Ita, mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babagana Monguno da ministoci 28 duk sun hallara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, shugaba Buhari ya nemi ministan sufuri, Rotimi Amaechi da takarwansa na sadarwa, Adebayo Shittu da su gabatar da addu’o’in bude taro, inda hakan yasa aka fashe da dariya a zauren majalisar.

KU KARANTA KUMA: Kujerar kakakin majalisa: Dogara ya ja baya daga tseren

A ranar Juma’a, 1 ga watan Maris ne mambobin majalisar suka kai ziyarar taya murna ga Shugaban kasar, a taron Shugaban kasar ya bayyana cewa mulkinsa na biyu zai yi zafi sosai.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel