Kotu za ta saurari bukatar EFCC na kwace kadarorin Patience Jonathan a watan Afrelu

Kotu za ta saurari bukatar EFCC na kwace kadarorin Patience Jonathan a watan Afrelu

- Kotu za ta saurari bukatar EFCC na kwace kadarorin Patience Jonathan a ranar 12 ga watan Afrelu

- A ranar 28 ga watan Fabreru, kotu ta dage sauraron karar inda ta ce akwai rudani a hujjojin da EFCC ta gabatar, wanda ta bukaci hujjojin baki

- EFCC ta bukaci kotu ta bata damar kwace akalla $8.4m da kuma N7.4bn da ke da alaka da tsohuwar uwar gidan shugaban kasa, Patience Jonathan

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Legas, a ranar Laraba, ta sanya ranar 12 ga watan Afrelu a matsayin ranar da za ta saurari bukatar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC na kwace akalla $8.4m da kuma N7.4bn da ke da alaka da tsohuwar uwar gidan shugaban kasa, Patience Jonathan.

Mai shari'a Mojisola Olatoregun ya yanke hukunci kan shari'ar da aka gudanar a ranar 28 ga watan Fabreru na bukatar kwace kadarorin, cewa akwai rudani a cikin hujjojin da aka gabatar, wanda za a iya magancewa idan bangarorin biyu sujka gurfana gaban kotun domin kare kawunansu.

KARANTA WANNAN: Duniya ina za ki da mu: An sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a jihar Filato

A halin yanzu an dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Maris domin sauraron hujjojin baki daga bangarorin guda biyu.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa kotun ta gaza ci gaba da sauraron karar a ranar Laraba, yayin da aka sanya ranar 12 ga watan Afrelu a matsayin ranar ci gaba da shari'ar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel