Yanzu: Kananan yara sun mutu, wasu sun makale a yayin da gini ya rubza a Legas

Yanzu: Kananan yara sun mutu, wasu sun makale a yayin da gini ya rubza a Legas

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa wani gini mai hawa ukku da ke yankin Itafaji, tsibirin Legas ya rubza a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa tashin hankali da rudani tsakanin al'ummar da ke zaune a kusa da ginin.

Channels TV ta ruwaito cewa akwai wata makarantar Firamare da ke a hawa na ukku na ginin, inda ake tsammanin daliban makarantar sun mutu, yayin da wasu har yanke ke a cikin ginin ba tare da samun hanyar fita ba.

Akalla dalibai 70 suka ke cikin makaratar amma zuwa yanzu, an ceto yara uku.

KARANTA WANNAN: Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope

Rahotanni sun bayyana cewa ginin dai yana a matsayin gidan zaman jama'a ba wai na kasuwanci ba, wanda ke dauke da bangarori da dama a ciki.

A halin yanzu dai jami'an hukumomin kai agajin gaggawa na ci gaba da kai dauki ga wadanda lamarin ya shafa da kuma yunkurin ceto wadanda suka makale.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel