Kujerar kakakin majalisa: Dogara ya ja baya daga tseren

Kujerar kakakin majalisa: Dogara ya ja baya daga tseren

- Hasashe sun nuna cewa Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ja baya daga tseren kujerar da ya ke kai a yanzu

- Hakan baya rasa nasaba da sahihan abubuwan da ke kewaye da jam’iyyarsa ta PDP a zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da aka kammala

Alamu sun nuna cewa ba lalllai be kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sake neman matsayin da yake kai ba a yanzu.

Hakan baya rasa nasaba da sahihan abubuwan da ke kewaye da jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP), a zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da aka kammala.

Kujerar kakakin majalisa: Dogara ya ja baya daga tseren
Kujerar kakakin majalisa: Dogara ya ja baya daga tseren
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne bayan majalisar wacce ta dawo hutu ta dage zamanta zuwa ranar Laraba domin karrama abokan aikinsu da suka rasa ransu, Hon. Temitope Olatoye Shuga, daga jihar Oyo da kuma Hon. Bethel Amadi daga jihar Imo.

Da yake magana da jaridar Independent, wani majiyi da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa ba zai sake Neman kujerar kakakin majalisa ba a majalisar kasar na yara.

KU KARANTA KUMA: Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope

Ku tuna Dogara ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki a watan Satumban 2018 ya nemi kujerar takara na wakiltan mazabunsu Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na jihar Bauchi a karo na biyu, bayan sun babe da gwamnan jihar Mohammed Abubakar kan banbancin siyasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel