CUPP ta zargi Buhari da hannu cikin zaben Alkalai 5 da zasu saurari shari’arsa da Atiku

CUPP ta zargi Buhari da hannu cikin zaben Alkalai 5 da zasu saurari shari’arsa da Atiku

Hadakar jam’iyyun adawar Najeriya, CUPP, ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da hannu cikin zabo manyan Alkalan kotun daukaka kara guda biyar da zasu saurari korafe korafen da abokin takararsa a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar zai shigar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito CUPP ta zargi shugabar kotun daukaka kara, Mai sharia Zainab Bulkachuwa da mika ma shugaban kasa sunayen Alkalai 8 da ta zaba don sauraron karar da Atiku ya shigar gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, inda daga bisani shugaban kasa ya amince da guda 5.

KU KARANTA: Adadin yan majalisun da jam’iyyun APC da PDP suke dasu a majalisar wakilai

Kaakakin CUPP, Ikeng Imo Ugochinyere ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, inda yace “Yan Najeriya zasu iya tuna cewa mun yi korafi kan yadda jam’iyyar APC ta bayar da kyautan kujerar Sanata ga mijin shugaban kotun daukaka kara, Zainab Bulkachuwa.

“Muna zargin akwai wata manufa da tasa APC ta baiwa mijin Bulkachuwa takarar Sanata bayan ba dashi aka yi zaben fidda gwani ba, don haka muke ganin hakan baya rasa nasaba da kokarin ganin Bulkachuwa ta nada lauyoyin da shugaban kasa ya amince dasu don sauraron karar da Atiku ya shigar a gaban kotun.

“Muna sane da cewa rashin samun kwatan kwacin wannan dama daga Alkalin Alkalan Najeriya ne tasa gwamnati ta daura masa karan tsana babu gaira babu dalili, saboda ya dage akan yin gaskiya kawai.” Inji CUPP.

CUPP ta cigaba da cewa tana da labarin daga cikin Alkalai guda 5, gwamnati ta hada baki da Alkalai guda 3 ta yadda duk irin kwararan hujjojin da Atiku zai baje musu ba zasu taba bashi gaskiya ba, Buhari zasu ba gaskiya a shari’ar.

Hakanan ta lissafa sunayen Alkalan guda biyar da suka hada da Zainab Adamu-Bulkachuwa Abdu-Aboki, Peter O. Ige, J. S. Ikyegh da mai sharia S. C. Oseji. Bugu da kari CUPP ta nemi Zainab Bulkachuwa, Aboki da Peter Ige dasu cire kansu daga sauraron karar Atiku Abubakar saboda ba zasu yi masa adalci ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel