Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope

Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope

- Wani tsohon ministan zirga zirga, Ebenezer Babatope, ya koka kan yadda hukumar zabe ta bayyana zaben jihar Kano a matsayin zaben da bai kammala ba

- Ebenezer Babatope ya jaddada cewa murde zabin al'ummar ta karfin tsiya zai iya haddasa rikicin da zai fi karfin Nigeria

- Bayan tattara sakamakon zaben, Abba Yusuf na PDP, ya samu kuri'u 1,014,474, yayin da Abdullahi Ganduje na APC ya samu kuri'u 987,810

Wani tsohon ministan zirga zirga, Ebenezer Babatope, ya koka kan yadda hukumar zabe ta bayyana zaben jihar Kano a matsayin zaben da bai kammala ba, yana mai cewa murde zabin al'ummar ta karfin tsiya zai iya haddasa rikicin da zai fi karfin Nigeria.

A cikin wata zantawa da jaridar INDEPENDENT, Mr Babatope ya gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da ta guji sauya sakamakon zaben da za a sake gudanar a jihar Kano, wanda ya bayyana a matsayin 'kowa ya iya allonsa ya wanke'.

Mr Babatope ya ce murde zaben jihar Kano zai iya zama babbar musiba ga Nigeria da kuma kawo karshen zaman lafiya a kasar, yana mai cewa duk wani mummunan mataki da aka dauka akan sakamakon zaben zai kawo rudani a Afrika da ma sauran kasashen duniya.

KARANTA WANNAN: El-Rufai ya nada Hadiza Balarabe a matsayin shugabar kwamitin mutane 38

Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope
Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope
Asali: UGC

Ya ce: "Ina rokon Allah ya sa kar INEC ta murde zabukan da za a sake gudanarwa, musamman a jihar Kano. Idan kuwa har suka kuskura suka yi, to kuwa za su jefa zaman lafiyar kasar da ma hadin kai cikin wani mummunan yanayi.

"Akwai rikitattun al'amura da suka dabaibaye zaben jihar Kano wanda ya ke bukatar taka-tsan-tsam. La'akari da abubuwan da aka fada da kuma wanda aka aikata, har yanzu Nigeria kasarmu ce kuma hadin kanta shine mafi a'ala ga kasar, Afrika da ma duniya baki daya.

"Kano wata babbar cibiyar siyasar kasar ce, idan kuma har suka yi wasa da hakan, tokuwa za su kashe zaman lafiyar Nigeria, kuma hakan zai haddasa babban rkici."

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa a daren ranar Litinin, hukumar zaben kasa INEC ta bayyana zaben jihar Kano a matsayin zaben da bai kammala ba.

Sai dai bayan tattara sakamakon zaben, Abba Yusuf na jam'iyyar PDP, ya samu kuri'u 1,014,474, yayin da gwmanan jihar mai ci Abdullahi Ganduje na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 987,810, inda aka samu tazarar kuri'u 26,655 a tsakanin 'yan takarar guda biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel