El-Rufai ya nada Hadiza Balarabe a matsayin shugabar kwamitin mutane 38

El-Rufai ya nada Hadiza Balarabe a matsayin shugabar kwamitin mutane 38

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya amince da nadin Hadiza Abubakar, zababbiyar mataimakiyarsa a matsayin shugabar kwamitin mutane 38

- Rahotanni sun bayyana cewa aikin kwamitin shine shirya ayyukan da gwamnatin jihar za ta gudanar yayin shiga ofis a karo na biyu

- El-Rufai ya samu nasarar sake lashe zaben gwamnan jihar a ranar 9 ga watan Maris, inda ya samu kuri'u 1,045,427

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya amince da nadin Hadiza Abubakar, zababbiyar mataimakiyar gwamnan jihar a matsayin shugabar kwamitin mutane 38 da ya kafa domin daukar nauyin dukkanin abubuwan da za su gudana na kama ragamar mulkinsa karo na biyu a jihar.

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Samuel Aruwan, mai magana da yawun gwamnan, ya ce aikin kwamitin shine shirya ayyukan da gwamnatin jihar za ta gudanar yayin shiga ofis a karo na biyu.

El-Rufai ya samu nasarar sake lashe zaben gwamnan jihar a ranar 9 ga watan Maris, inda ya samu kuri'u 1,045,427 da ya ba shi damar lallasa dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP, Isa Ashiru wanda ya samu kuri'u 814,168.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: A yau majalisar dattijai za ta soma tafka muhawara kan kasafin 2019

El-Rufai ya nada Hadiza Balarabe a matsayin shugabar kwamitin mutane 38
El-Rufai ya nada Hadiza Balarabe a matsayin shugabar kwamitin mutane 38
Asali: UGC

Mambobin kwamitin sun hada da Emmanuel Jekada, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kaduna, zababbun sanatoci guda biyu, Suleiman Abdu Kwari da Uba Sani, da kuma Zainab Ahmed, ministar kudi.

Sauran sun hada da Idris Othman, Husaini Adamu Dikko, Charles Bonat, tsohon sakataren gwamnatin jihar; Hafsat Baba, kwamishiniyar mata da bunkasa rayuwar al'ummar jihar; Kabir Mato, kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya; Muhammad Abdullahi, kwamishinan tsare tsare da kasafin kudin jihar da kuma Ben Kure, babban daraktan ofishin yakin zaben jam'iyyar APC na jihar Kaduna.

Haka zalika daga cikin wadanda suke cikin kwamitin mutane 38 akwai Muhammad Bello da Sani Sidi, tsohon babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar NEMA.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel