Jam'iyyar APC ta bada satar amsar yadda zata fiddo da shugabannin majalisar tarayya

Jam'iyyar APC ta bada satar amsar yadda zata fiddo da shugabannin majalisar tarayya

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Najeriya Hon. Femi Gbajabiamila ya bayar da haske akan yadda shugabancin majalisa zai kasance a wannan karon inda yace jam'iyyar su All Progressives Congress (APC) ce zata zabi wadanda za su shugabance su.

Sai dai kuma shugaban na masu rinjaye ya bayyana cewa duk da dai ya zuwa yanzu jam'iyyar ta su bata fara tattaunawa akan kujerun da kuma matsayin da za'a baiwa kowa ba a matakin ta, yana da yakinin cewa daga karshe duk abun da ta yanke haka za'ayi.

Jam'iyyar APC ta bada satar amsar yadda zata fiddo da shugabannin majalisar tarayya
Jam'iyyar APC ta bada satar amsar yadda zata fiddo da shugabannin majalisar tarayya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari zai kara gina rijiyoyin mai 37

Legit.ng Hausa ta tuna cewa kimanin shekaru hudu da suka gabata dai uwar jam'iyyar bata sa baki ba wajen zabar shugabannin majalisar wanda hakan ne ya sa ma wasu suka lashe kujerun da da yawun ta ba.

Masu sharhi kan al'amurran siyasa dai daga baya sun yi ta alakanta yadda alakar bangaren majalisa da na masu zartaswa ta rika samun tasgaro akan wannan matsar da ta auku tun farko wadda kuma suke son magancewa a wannan karon.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta rukunin kamfanonin albarkatun man fetur mallakin gwamnatin tarayya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) ta sanar da fara daukar aiki a hukumar a fannoni da dama kwanaki kadan bayan kammala zabukan 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel