Da duminsa: A yau majalisar dattijai za ta soma tafka muhawara kan kasafin 2019

Da duminsa: A yau majalisar dattijai za ta soma tafka muhawara kan kasafin 2019

- A yau ne ake sa ran majalisar dattijai za ta soma fara tafka muhawa kan kasafin kudin 2019 na kasar da ya kai kimanin N8.83

- Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan, Ahmad Lawan ne zai jagoranci muhawarar, inda ake sa ran sauran sanatocin za su tofa albarkacin bakinsu

- Haka zalika Saraki ya umurci kwamitin albashi mafi karanci ya tabbata ya gabatar da rahotonsa gaban majalisar ya ranar Talata ta satin sama

Rahotanni sun bayyana cewa a yau ne ake sa ran majalisar dattijai za ta soma fara tafka muhawa kan kasafin kudin 2019 na kasar da ya kai kimanin N8.83.

A ranar 19 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kiyascin kasafin kudin kasar gaban hadakar majalisun tarayyar kasar da suka hada da majalisar dattijai da ta wakilan tarayya.

Sanatoci ba su samu damar duba kasafin kudin ba kasancewar sun je hutu tun watan Janairu domin baiwa 'yan majalisun damar shiga harkokin yakin zaben 2019. Sai dai, shugaban majalisar dattijan, Bukola Saraki a zaman da majaisar ta yi jya ya sanar da cewa a yau ne za a soma tafka muhawara kan kasafin kudin.

KARANTA WANNAN: Sharhi: Muhimman bayanai game da Mai Mala Buni, sabon gwamnan Yobe

Da duminsa: A yau majalisar dattijai za ta soma tafka muhawara kan kasafin 2019
Da duminsa: A yau majalisar dattijai za ta soma tafka muhawara kan kasafin 2019
Asali: UGC

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan, Ahmad Lawan (APC, Yobe), shine zai jagoranci muhawarar, inda ake sa ran sauran sanatocin za su tofa albarkacin bakinsu.

A wani labarin makamancin wannan, Saraki ya baiwa kwamitin albashi mafi karanci na ma'aikatan kasar da ya tabbata ya gabatar da rahotonsa gaban majalisar ya ranar Talata ta satin sama.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa tuni dai majalisar wakilan tarayya ta amince da N30,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci, inda ake zaman jiran majalisar dattijai ta bayyana nata matsayar.

Sai dai ita majalisar zartaswar kasar ta gabatar da N27,000 a matsayin albashi mafi karanci da za ta iya biyan ma'aikatan kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel