Allura-cikin-ruwa: Hukumar NNPC ta shelanta fara daukar sabbin ma'aikata

Allura-cikin-ruwa: Hukumar NNPC ta shelanta fara daukar sabbin ma'aikata

Hukumar nan ta rukunin kamfanonin albarkatun man fetur mallakin gwamnatin tarayya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) ta sanar da fara daukar aiki a hukumar a fannoni da dama kwanaki kadan bayan kammala zabukan 2019.

Hukumar dai kamar yadda muka samu, ta bayyana hakan ne a shafukan ta na sada zumuntar zamani irin su Facebook da Tuwita da kuma shafin su na yanar gizo inda suka bukaci dukkan mai bukata ya hanzarta yin rijista.

Allura-cikin-ruwa: Hukumar NNPC ta shelanta fara daukar sabbin ma'aikata
Allura-cikin-ruwa: Hukumar NNPC ta shelanta fara daukar sabbin ma'aikata
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Jerin rumfunan da za'a sake yin zabe a jihar Kano

Legit.ng haka zalika ta samu cewa hukumar ta Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) ta kuma gargadi mutane da cewa ita ba zata karbi ko da sisin kobo ba daga masu sha'awar samun aiki a kamfanin, komai kyauta ne.

A saman shafin na su kuwa na yanar gizo, mun ga cewa akwai taswirar da aka tsara na yadda za'a iya yin rijistar ga masu sha'awa kuma a akwai bangarori da dama kama daga na masu shaidar kammala karatun digiri har ya zuwa kasan su da ma kuma masu wadanda suka fi hakan.

Kamfanin na NNPC dai ya shiga bakunan mutane sosai musamman ma a lokacin yakin neman zaben shugabancin kasar nan da ya gabata inda dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce sai sayar da shi idan ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel