Aiki-dai-aiki-dai: Shugaba Buhari zai kara gina sabbin rijiyoyin mai 37

Aiki-dai-aiki-dai: Shugaba Buhari zai kara gina sabbin rijiyoyin mai 37

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da albarkatun mai fetur watau Depertment for Petroleum Resources (DPR) ta sanar da cewar, an amince mata da samar da jimlar karin rijiyoyin mai guda 37 a sassa daban daban na Najeriya.

Wannan matakin da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin an dauke shi ne domin kasar Najeriya kara yawan danyen man fetur din da ake sarrafawa ya zuwa akalla ganguna 189,850 a kullum.

Aiki-dai-aiki-dai: Shugaba Buhari zai kara gina sabbin rijiyoyin mai 37
Aiki-dai-aiki-dai: Shugaba Buhari zai kara gina sabbin rijiyoyin mai 37
Asali: UGC

KU KARANTA: Ganduje ya tafi Abuja neman a tsige Kwamishina Wakili

Legit.ng Hausa ta samu labari daga majiyar mu cewar, daga cikin ribiyoyin man guda 37 da za'a sake gidanawa, guda 29 an sanya su ne a sahun samar da ci gaban kasa, inda kuma hukumar ta DPR ta ware sauran guda 8 da aka hada su a guri guda.

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin kundin ta na kwanan na na nasarorin data samu a shekarar 2018, wanda wakilinmu ya samo daga gunt Ma’akatar Mai da Albarkatu dake garin Abuja a ranar Juma’ar data gabata.

Hukumar ta ci gaba da cewa, an kuma wanzar da bayar da lasisin sarrafa mai na kan tudu ta hanyar yin amfani da yanar gizo, inda kuma amincewr akayi ta ta hanayar sanya ido ta ROMS da tsarin defo-defo da tsarin shigowa da fitarwa ta EPS data LBPS da kuma ta ROS.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel