Yabon gwani: Sarkin Kano ya jinjinawa Kwamishinan 'yan sanda CP Wakili

Yabon gwani: Sarkin Kano ya jinjinawa Kwamishinan 'yan sanda CP Wakili

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ya yi godiya ta musamman ga Kwamishinan 'Yan Sandan jihar CP Mohammed Wakili da sauran jami'an tsaro kan irin rawar da suka taka wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar yayi takaddamar zaben gwamna da ya gabata.

Wannan jinjina da yabon dai na zuwa ne a cikin wata fita da manema labarai da sairkin yayi a fadar sa bayan da aka gudanar da zaben gwamnoni da kuma 'yan majalisar jiha a fadin kasar a ranar 9 ga watan Maris.

Yabon gwani: Sarkin Kano ya jinjinawa Kwamishinan 'yan sanda CP Wakili
Yabon gwani: Sarkin Kano ya jinjinawa Kwamishinan 'yan sanda CP Wakili
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Sabon gwamnan jihar Zamfara

Sarkin ya bayyana cewa hukumar INEC ce kadai ke da 'yancin bayyana sahihin sakamakon zabe, inda hukumar ta bayyana cewa zaben bai kammala ba, kuma akwai wasu mazabu da za a sake zabe a jihar.

Daga nan, sarkin sai ya yi kira ga al'ummar Kano da su zauna lafiya kuma su kwantar da hankali da kuma kiyaya yada jita jita.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jami'an 'yan sandan na jihar Kano karkashin jagorancin shugaban na su sun kama mataimakin gwamnan jihar da kwamishin kananan hukumomi da ma shugaban karamar hukumar hukumar Nasarawa da laifin kokarin yin magudi.

Wannan dai ya ja ma 'yan sandan farin jini sosai inda ake cigaba da yaba masau musamman ma ganin yadda ba kasafai ake kama masu rike da mukamai ba da laifi a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel