Gwamnatin Kaduna ta kaddamar da dokar tabaci a kananan hukumomi guda 2

Gwamnatin Kaduna ta kaddamar da dokar tabaci a kananan hukumomi guda 2

Gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da kaddamar da dokar hana shiga da fita a wasu kananan hukumomin jahar guda biyu don shawo kan wasu tashin tashina da hare hare da aka yi fama dasu a wadannan yankuna na jahar.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin gwamnatin jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka yayin wata hira da aka yi dashi a gidan rediyon gwamnatin jahar Kaduna, KSMC, da safiyar Laraba, 13 ga watan Maris.

KU KARANTA: Ba yau farau ba: Jerin wasu manyan zabuka 6 da basu kammalu ba tun daga shekarar 2011

A jawabinsa, Samuel ya bayyana cewa dokar hana shige da ficen ya shafi kananan hukumomi guda biyu ne kacal na jahar Kaduna, karamar hukumar Kajuru, da karamar hukumar Chikun.

Gwamnatin ta sanya dokar hana shige da fice a kafatanin karamar hukumar Kajuru tun daga karfe 6 na yamma har zuwa karfe 6 na safe, har sai yadda hali da yayi, haka zalika ta sanya dokar hana shige da fice a garuruwan Kujama da Maraban Rido na karamar hukumar Chikun, suma daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe.

Do haka ake kira ga jama’a mazauna karamar hukumar Kajuru, garin Maraban rido da Kujama na karamar hukumar Chikun dasu baiwa gwamnati da jami’an tsaro hadin kai ta hanyar yin biyayya ga doka da oda a wannan lokaci.

Gwamnati ta dauki wannan mataki ne don ta samar da dawwamammen zaman lafiya a yankunan nan da ma jahar baki daya, ba wai don kuntata ma al’umma mazauna yankin ba, Allah ya bamu zaman lafiya ai daurewa a Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel