Ba yau farau ba: Jerin wasu manyan zabuka 6 da basu kammalu ba tun daga shekarar 2011

Ba yau farau ba: Jerin wasu manyan zabuka 6 da basu kammalu ba tun daga shekarar 2011

Sakamakon sanar da rashin kammaluwar zabukan gwamnoni a wasu jahohin Najeriya, musamman ma zaben gwamnan jahar Kano da yafi daukan hankali, yasa jama’a nata tofa albarkacin bakinsu game da lamarin, sai dai yawanci tir suke yi da wannan mataki na hukumar INEC.

Don haka Legit.ng ta binciko wasu zabukan gwamnoni da ma wadanda bana gwamnoni ba da hukumar INEC ta taba gudanarwa a baya wadanda basu kammala ba, kuma daga bisani ta maimaita zabukan har sai da aka samu wanda yayi nasara.

KU KARANTA: Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki

Wani mai muhimmanci shine dalilin da yasa INEC take sanar da zabe bai kammala ba shine idan har ya kasance bambamcin dake tsakanin yan takara biyu dake kan gaba, bai kai adadin kuri’un da aka soke ba, ko don rikici daya tashi, lalata kuri’a ko kuma don kuri’un da aka kada a akwati sun fi adadin masu zaben.

Ga wasu daga cikin zabukan da aka samu irin wannan matsala;

Zaben Sanatan Anambra 2011

Dora Akunyili( APGA) —— 66,273

Chris Ngige ( ACN) ——65,576

Bambanci —697

Kuri’un da aka soke——7,930

Zaben gwamnan jahar Anambra 2013

Obiano ( APGA) —174,710

Tony Nwoye ( PDP) — 94,956

Bambanci ——-79,754

Kuri’un da aka soke——113,113

Zaben gwamnan jahar Imo 2015

Okorocha( APC) —385,671

Ihedioha( PDP) ——306,142

Bambanci ———79,529

Kuri’un da aka soke —— 144,715

Zaben gwamnan jahar Kogi 2015

Abubakar Audu( APC) —-240,867

Wada Idris ( PDP) —199,514

Bambanci —————41,353

Kuri’un da aka soke ———49,953

Zaben gwamnan jahar Bayelsa 2015

Dickson ( PDP) ——-105,748

Sylva ( APC)——72,594

Bambanci ——-33,154

Kuri’un da aka soke ---- 120,000

Zaben gwamnan jahar Osun 2018

Ademola Adeleke (PDP) ------ 254,698

Gboyega Oyetola (APC) ------- 254,345

Bambanci ---------353

Kuri’un da aka soke ----- 3,498

Da wannan za’a iya gane cewa babu wata manakisa da INEC ke shiryawa kamar yadda wasu ke zarginta don ta sanar da zabukan gwamnonin jahohin Kano, Bauchi, Adamawa, Benuwe, Sakkwato da Filato a matsayin wadanda basu kammalu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel