Buhari ya nada mataimakinsa jagorantar kwamitin binciken ayyukan gwamnati

Buhari ya nada mataimakinsa jagorantar kwamitin binciken ayyukan gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo shugaban wani kwamitin bincike daya kafa domin gudanar da cikakken bincike akan ayyukan da gwamnatin tarayya take gudanarwa, da kuma duk tsare tsaren data kirkiro.

Legit.ng ta ruwaito ofishin sakataren gwamnatin tarayya ce ta sanar da haka a ranar Talata, 12 ga watan Maris, inda tace Buhari ya shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari don yayi aiki tare da Osinbajo a wannan kwamiti.

KU KARANTA: Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki

Bukatar shugaban kasa ga wannan kwamiti shine su tabbatar da matsayin da ayyukan da gwamnati ke gudanarwa suka kai, musamman ayyukan data gada daga gwamnatocin baya da kuma ayyukan da ta kirkiro, da kuma tsare tsare.

Hakanan ya umarci kwamitin data lalubo duk wasu kalubale da za’a iya fuskanta a kokarin cigaba da gudanar da wadannan ayyuka da tsare tsare, tare da hanyoyin shawo kan kalubalen, daga karshe ya bukaci kwamitin ta samar da kundin da zata zamto manuniya ga sababbin ministocin da Buhari zai nada game da inda gwamnatin ta dosa.

Mambobin wannan kwamiti sun hada da shugaban ma’aikatan Najeriya, gwamnan babban bankin Najeriya, Ministan kasafin kudi da tsare tsare, Ministan ayyuka, lantarki da gidaje, Ministan kudi, Ministan shari’a, Ministan kasuwanci, Ministan sufuri, Ministan noma, Ministan ruwa.

Sauran sun hada da mashawarcin shugaban kasa akan harkar tsaro, babban sakataren majalsar zartarwa, da kuma mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel