A cikin Kano Kwamishinan ‘Yan Sanda M. Wakili zai ajiye aiki

A cikin Kano Kwamishinan ‘Yan Sanda M. Wakili zai ajiye aiki

A jiya ne rade-radi ya fara yawo cewa ana nema ko har an kai ga tsige Kwamishinan ‘Yan Sandan Najeriya na Jihar Kano watau Mohammed Wakili. Yanzu dai mun fahimci cewa babu gaskiya a maganar.

Kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar DAILY NIGERIAN, wasu manyan jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da cewa maganar yunkurin sauke Kwamishinan na jihar Kano ba gaskiya bane domin babu dalili na yin hakan a yanzu.

Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar da cewa CP Mohammed Wakili zai ajiye aiki ne nan da ‘yan kwanaki kadan a tsakiyar Watan Mayun bana. Hakan zai zama dole ne a sanadiyyar cewa ya cika shekaru 60 yana aikin tsaro.

Kwamishina Mohammed Wakili yayi wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya aiki na tsawon shekaru 32, don haka zai yi ritaya a lokacin da ake daf da kafa gwamnati a Najeriya. Majiyar tace Wakili zai cigaba da aiki a Kano har wannan lokaci.

KU KARANTA: Abin da ya sa APC ta yi wa PDP mummunan kayi a zaben Legas

A cikin Kano Kwamishinan ‘Yan Sanda M. Wakili zai ajiye aiki
Da wuya a cire Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano
Asali: Facebook

Bisa dukkan alamu dai gwamnatin jihar Kano za ta nemi a maye gurbin Mohammed Wakili da wani jami’in. CP Mohammed Wakili yayi bakin kokarin sa wajen ganin hana ‘yan siyasa tafka magudi a zaben gwamna na Jihar Kano da ake yi.

Wannan ya sa masu mulkin jihar ke ganin Kwamishinan na ‘yan sanda ya zama masu alaka-ka-kai don haka su ke neman a canza masa wurin aiki, hakan zai bada dama ayi amfani da jami’an tsaron wajen murde zaben da za a karasa a jihar.

Daga cikin wadanda su ka yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje rakiya zuwa Abuja wajen ganin an sauke M. Wakili su ne: Shugaban majalisar Kano Kabiru Rurum da Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas da kuma Alhaji Nasiru Aliko-Koki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel