Atiku: Tawagar lauyoyin PDP sun dira ofishin INEC

Atiku: Tawagar lauyoyin PDP sun dira ofishin INEC

Emeka Etiaba, babban lauyan dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da tawagar sa sun dira ofishin kwamishinan harkokin shari’a na hukumar zabe ta kasa (INEC) dauke da takardar hukuncin kotu na bawa PDP damar gudanar da binciken kayan aikin zaben shugaban kasa da INEC ta yi amfani da su.

Kotun daukaka kara ta umarci hukmar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta bawa dan takarar shugaban kasa da aka kayar a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar, da jam’iyyar sa, PDP, damar duba dukkan kayayyaki da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin Abdul Aboki ta ce INEC ta bawa Atiku da PDP damar yin nazari da binciken kwakwafi a kan dukkan kayan da aka yi amfani da su a zaben.

Da ya ke karanto hukuncin da kotun ta yanke bisa amincewar alkalan uku, Mista Aboki, ya hana Atiku da PDP gudanar da bincike ta hanyar kimiyyar zamani (Forensic analysis) a kan kayan aikin zaben da INEC za ta ba su don su duba. Kazalika, kotun ta hana INEC bayar da kayan aikin zaben domin gudanar da bincike ta hanyar kimiyyar zamani a kan su.

Atiku: Tawagar lauyoyin PDP sun dira ofishin INEC
Shugabannin jam'iyyar PDP yayin zanga-zanga a ofishin INEC
Asali: UGC

Hari la yau, kotun ta hana masana bincike ta hanyar kimiyyar zamani su duba kayan aikin zaben, musamman fom din EC48 da wasu ragowar kayayyakin kamar yadda ma su shigar da kara su ka nema.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 55, sun kubutar da mutane 760 a Zamfara

Atiku da PDP sun tafi kotu ne domin kalubalantar sakamakon zaben da INEC ta bayyana sunan shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara.

INEC ba ta bayyana lokacin da zata bawa jam’iyyar ta PDP damar duba kayan aikin zaben shugaban kasar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel