Da dumin sa: Ganduje ya ruga Abuja neman a cire kwamishinan 'yan sandan Kano

Da dumin sa: Ganduje ya ruga Abuja neman a cire kwamishinan 'yan sandan Kano

Biyo bayan takaddama a zaben gwamnan jihar Kano, Gwamna Ganduje ya yi tattaki zuwa Abuja don Neman a cire kwamishinan 'yansanda na jihar, Muhammad Wakili.

Majiyarmu ta Daily Nigerian ta bayyana cewa Muhammad Wakili ya yi kokarin daidaita lamura a lokacin zaben gwamna a jihar Kano.

Da dumin sa: Ganduje ya ruga Abuja neman a cire kwamishinan 'yan sandan Kano
Da dumin sa: Ganduje ya ruga Abuja neman a cire kwamishinan 'yan sandan Kano
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin rumfunan da za'a sake zabe a jihar Kano

Bayanai sun nuna gwamnan ya samu rakiyar shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Rurum da shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.

A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta cire sunan gwamnan jihar Imo, dan jam'iyyar APC mai suna Rochas Okorocha daga jerin sunayen Sanatocin da suka samu nasara a zaben da ya gudana.

Kamar yadda muka samu, hukumar zaben ta Independent National Electoral Commission (INEC) ta saka sunayen wadanda suka samu nasa a zabukan shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya a shafin ta na yanar gizo da ta ce za ta baiwa satifiket.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel