Sojoji sun yi ram da barayin akwatin zabe 24 a jihohin Imo, Abia da Rivers

Sojoji sun yi ram da barayin akwatin zabe 24 a jihohin Imo, Abia da Rivers

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta yi ram da mutane 24 da suke da alaka da satar akwatunan zabe da garkuwa da mutane a jihohin Abia, Imo da kuma Rivers.

Mai Magana da yawun rundunar sojin, Sagir Musa ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a ranar Talata, 12 ga watan Maris inda ya kara da cewa sun kama mutane 15 daga cikin mutanen 24 a jihar Abia.

Ya ce daga cikin mutane 15 din da suka kama biyar Karen farautyar yan siyasa ne masu tayar da zaune tsaye a lokacin zabe.

Sojoji sun yi ram da barayin akwatin zabe 24 a jihohin Imo, Abia da Rivers
Sojoji sun yi ram da barayin akwatin zabe 24 a jihohin Imo, Abia da Rivers
Asali: Depositphotos

Musa ya ce dakarun sojojin sun kama wasu mutane shida a hanyar Osisioma dauke da takardun zaben da aka riga aka dangwala su.

Bayan nan kuma sojojin sun kama wasu masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da wani ma’aikacin INEC.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kano: Nine zan yi nasara koda an sake zabe – Inji Abba gida-gida

A jihar Imo sojoji sun kama wasu sojojin bogi dake raka wata ‘yar siyasa a hanyar Everyday Super Market a Owerri.

A karshe Musa yace sojoji sun ceto wani mutum mai suna Authur Nkama a karamar hukumar Odukpani da aka yi garkuwa da shi a Ikot jihar Rivers.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel