Zaben Kano: Nine zan yi nasara koda an sake zabe – Inji Abba gida-gida

Zaben Kano: Nine zan yi nasara koda an sake zabe – Inji Abba gida-gida

Dan takarar kujurar gawamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba magoya bayansa tabbacin cewa shine zai yi nasara yayin sake zaben gwamna a jihar.

A wani jawabi dauke da sa hannun kakakin Abba, Sanusi Bature Dawakin Tofa yace “Mutanen Kano sun gani karara yadda wasu makiyan damokradiyya wadanda suka kasance masu matsayi a gwamnatin jihar Kano ciki harda mataimakin gwamna, Dr Nasiru Tusuf Gawuna, kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo da Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Alhaji Lamin Sani suka kai hari cibiyar hada kuri’u, wanda hakan yayi sanadiyar hana a kaddamar da PDP a matsayin mai nasara.”

Zaben Kano: Nine zan yi nasara koda an sake zabe – Inji Abba gida-gida
Zaben Kano: Nine zan yi nasara koda an sake zabe – Inji Abba gida-gida
Asali: Twitter

Dawakin Tofa yayi zargin cewa PDP na sane da takardun zabe 500 da ma’aikatar buge-buge ta jihar Kano ta buga sannan aka watsa su a fadin mazabun jihar, wanda daga ciki ne yan sanda suka kama kwalaye 10.

“Rokon mu ne ganin cewa an mika dukkanin masu laifin zabe kotu da wuri domin su fuskanci hukunci akan karya damokradiyya,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Ya roki dukkanin magoya bayan PDP da su kwantar da hankulansu cewa jam'iyyar na akan tafarkin kafa gwamnatin gaba a jihar Kano.

"Kada magoya bayanmu su manta cewa tuni PDP ce kan gaba a zaben karshe da aka kidaya, za a maimaita zaben ne a inda PDP ke da karfi. Kowa ya ci gaba da sa ran nasara," inji shi.

Ya bukaci masu zabe a yankunan da abun ya shafa da su fito kwansu da kwarkwatansu domin zabar PDP a lokacin gudanar da zaben maimaicin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel