Nasarar Buhari: Jarumin Kannywood zai cika alkawarin da ya dauka

Nasarar Buhari: Jarumin Kannywood zai cika alkawarin da ya dauka

- Jarumin Kannywood, Bello Muhammed ya ce cika alkawarin da ya dauka na aske suman kansa muddin Buhari ya zarce

- Jarumin wanda yana daya daga cikin magoya bayan Buhari ya dauki wannan alkawarin ne domin murnar zarcewar Buhari

- Bello Muhammad ya ce a garin Kaduna za ayi askin kuma gwamna Nasir El-Rufai zai kasance sheda a ranar da za a bayyana nan gaba

Nasarar Buhari: Jarumin Kannywood zai cika alkawarin da ya dauka
Nasarar Buhari: Jarumin Kannywood zai cika alkawarin da ya dauka
Asali: Twitter

Jarumin Kannywood, Bello Mohammed ya ce zai aske sumar kansa da aka dade da saninsa da shi domin cika alkawarin da ya dauka na yin hakan idan har shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zabe.

Mr Muhammad ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Instagram, generalbmb4pmb inda ya ce a garin Kaduna za ayi masa askin.

DUBA WANNAN: An damke wanda ake zargi da kashe dan majilisar tarayya a Oyo

Jarumin dan asalin jihar Filato yana daya daga cikin jaruman da suka taka rawar gani wurin yiwa jam'iyyar All Peoples Congress (APC) yakin neman zabe kuma an san yana daga cikin masu goyon bayan Buhari.

A cikin faifan bidiyon da ya saki a shafinsa na Instagram din, ya ce gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai zai kasance a wurin da za ayi masa askin domin ya sheda inda ya ce za a bayyana ranar da za ayi askin nan gaba.

A wani sako da ya wallafa, ya ce "Na dau alkawarin cewa zan aske gashin kai na da nake tinkaho dashi saboda nuna farin ciki na a kan samun nasarar zarcewar shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki."

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Muhammad Bello yana daya daga cikin jaruman Kannywood da suka yiwa shugaba Muhammadu Buhari yakin neman zabe domin ra'ayin kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel