2019: An yi mamakin yadda APC tayi watsa-watsa da PDP a Legas

2019: An yi mamakin yadda APC tayi watsa-watsa da PDP a Legas

Masu bibiyar harkar siyasa sun yi mamakin abin da ya faru a zaben gwamna da ‘yan majalisun dokoki da aka yi a jihar Legas. Mutane da-dama sun yi tunanin cewa PDP za tayi wani kokari a zaben.

Duk da cewa Legas ce gidan babban kusan jam’iyyar APC watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, an yi ta hasashen cewa jam’iyyar adawa ta PDP za ta ba APC mamaki a zaben gwamna na bana, ganin yadda siyasar kasar ke tafiya,

A zaben shugaban kasa da aka yi a 2015, jam’iyyar APC ta samu kuri’a 792, 460, inda shi kuma Goodluck Jonathan ya tashi da kuri’a 632, 327. Sai dai a zaben bana, ratar da ke tsakanin Shugaba Buhari da Atiku bai kai yawan ba 2015 ba.

Wannan yana cikin dalilan da ya sa jama’a su ka hango cewa sai APC tayi da gaske a zaben gwamna na bana. Haka zalika a 2015, lokacin da Jimi Agbaje ya kara da Akinwumi Ambode, APC ta iya tsira ne da tazarar kuri’u 152,206 rak.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya godewa Mutanen Kaduna da su ka zaben sa

2019: An yi mamakin yadda APC tayi watsa-watsa da PDP a Legas
'Dan takarar APC ya tika Agbaje na PDP da kasa a zaben Legas
Asali: Facebook

A zaben na bana kuwa, sai ga shi Jimi Agbaje na PDP ya samu kuri’a 206, 141, yayin da ‘Dan takarar APC mai mulki, Jide Sanwo-Olu ya lashe kuri’u fiye da 730, 000. An dai samu ratar kuri’un da sun haura 530, 000 a zaben gwamnan na bana.

Daily Trust ta bayana cewa daga cikin dalilan da su ka sa PDP ta kashi a wannan karo shi ne APC ta iya kokarin sulhunta rikicin da ke cikin gidan ta kafin zaben. Haka kuma APC ta yi kokarin jawo wadanda ke adawa da ita ana daf da zabe.

Jaridar tace nasarar da APC ta samu bai kuma rasa nasaba da mutanen Ibo da aka lallaba wannan karo su ka zabi Sanwo Olu. APC ta cin ma wannan nasara ne bayan da kungiyar Ohaneze ta Legas tayi wa jam’iyyar APC mubaya’a a zaben na 2019.

Haka nan kuma barakar da ke cikin PDP ya kara taimakawa wajen nakasa jam’iyyar adawar. Har sai da ta kai Jiga-jigan PDP irin su Adeseye Ogunlewe, su na kokawa da halin rashin hadin-kan da jam’iyyar ta shiga ciki, wannan ya ba APC nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel