Buhari ya gana da gwamnonin APC a Abuja

Buhari ya gana da gwamnonin APC a Abuja

Jim kadan bayan dawowar sa Abuja daga hutun zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da ya yi a garin Daura, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawa da wasu gwamnonin APC 7 a fadar sa, Villa.

Gwamnonin bakwai su ne; Yahaya Bello na jihar Kogi, Nasir El-Rufa’I na jihar Kaduna, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Abdulaziz Yari na jihar zamfara, Abubakar Badaru na jihar Jigawa, Kashim Shettima na jihar Borno da Fayemi Kayode na jihar Ekiti.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar ba a bayyana dalilin ganawar ba sannan gwamnonin sun ki cewa komai bayan kamala ganawar ta su da Buhari.

Sai dai, NAN, ta ce ta jiyo daga majiya mai tushe cewar batun zaben gwamnoni da aka kammala a jihohi 29 na kasar nan ne ya mamaye tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnonin da shugaban kasa.

Buhari ya gana da gwamnonin APC a Abuja
Buhari da gwamnonin APC
Asali: Twitter

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana sakamakon zaben jihohi 6 a matsayin ‘bai kammalu’ ba. Jihohin da abin ya shafa sune; Adamawa, Bauchi, Benuwe, Filato, Kano da Sokoto yayin da aka soke duk wata harkar maganar zabe a jihar Ribas.

DUBA WANNAN: Mata sun mamaye ofishin INEC Sokoto, sun bukaci a sanar da Tambuwal ya ci zabe

Ana sa ran INEC zata fitar da sabbin ranakun karasa zabe a jihohin 6 da matsalar ta shafa.

Daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC ma su ci da suka shiga rintsin karasa zabe a jihohinsu akwai Mohammed Abubakar na jihar Bauchi, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Simon Lalong na jihar Filato, da Jibrilla Bindow na jihar Adamawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel