APC, PDP da Jam’iyyu 7 ne kawai ke da wakilci a Majalisar Tarayya

APC, PDP da Jam’iyyu 7 ne kawai ke da wakilci a Majalisar Tarayya

Koda yake kundin doka ta bayar da dammar kafa jam’iyyun siyasa bila adadin, hakan bai sanya mafi akasarinsu tabuka wani abun a zo a gani ba a zaben Shugaban kasa da na majalisun dokokin kasar ba.

An yi wa sabbin jam’iyyu dai-dai har guda 91 rajista a zaben 2019, jam’iyyu tara ne kadai za su samar da wakilai a Majalisar Tarayya.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da sunayen zababbun ‘yan majalisar tarayya. Sai dai kuma akwai kujerun majalisar tarayya 20 da har yau da ba a bayyana ba, saboda rashin kammaluwar zaben su.

APC, PDP da Jam’iyyu 7 ne kawai ke da wakilci a Majalisar Tarayya
APC, PDP da Jam’iyyu 7 ne kawai ke da wakilci a Majalisar Tarayya
Asali: Twitter

Daga cikin kujerar wakilai 360, jam’iyyar APC na da 211, sai PDP mai guda 111.

Sauran jam’iyyu da za su samar da mambobin majalisar tarayya sun hada da APGA, guda shida. ADC uku, AA guda biyu sai PRP ita ma biyu.

KU KARANTA KUMA: Asha: An tsinci gawar matashi cikin rijiya a garin Jos

ADP, APM da kuma SDP kowace na da wakili daya. Akwai mata 10 daga cikin wadannan 300 da aka sanar da nasarar su.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa a yau, Talata, ne rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta gurfanar da Mista Uche Onyeaguocha, wakilin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP tare da wasu mutane uku a gaban wata kotun majistare da ke Owerri bisa zargin su da saba dokokin zabe.

Ragowar da aka gurfanar tare da Onyeaguocha su ne; Steve Asimobi, Paschal Onwukaike da Oliver Enwerenem.

Rundunar ‘yan sanda na tuhumar su da aikata laifuka 10 da ke da alaka da nuna halayen da basu dace ba lokacin zabe, lalata kayan aikin zabe, hana zabe gudana da kuma yaga takardun sakamakon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel