Kungiyar Boko Haram ta shiga tsaka mai wuya, kayayakinsu sun kare - MNJTF

Kungiyar Boko Haram ta shiga tsaka mai wuya, kayayakinsu sun kare - MNJTF

Sojojin hadin gwiwa na MNJTF a Jamhuriyar Chadi sun ce shugabanin kungiyar Boko Haram sun shiga halin tsaka mai wuya a halin yanzu.

Kakakin MNJTF, Timothy Antigha ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranara Talata a babban birnin tarayya, Abuja.

Kwanel Antigha ya ce kungiyar tana shiga matsatsi bayan hare-haren sama da na kasa da dakarun sojoji na Operation Yancin Tafki da ke tafkin Chadi suka rika kai musu cikin kwanan-kwanan nan.

Ya kuma ce tsaffin mayakan kungiyar da suka tuba sun ce an karya lagwan mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Mr Antigha ya kara da cewa hakan ya faru ne saboda hana su sakat da sojojin su kayi tare da rashin samun abinci, magunguna da makamai.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda Gwamna Bello ya yi murnar lashe zabe cikin sabon salo mai kayatarwa

'Yan Boko Haram suna cikin mawuyacin hali, kayan abincinsu ya kare - MNJTF
'Yan Boko Haram suna cikin mawuyacin hali, kayan abincinsu ya kare - MNJTF
Asali: UGC

Kakakin na MNJTF ya ce daya daga cikin dabarun yaki da rundunar ke amfani dashi sun hada da nemo bayanan sirri cikin dare da rana ta hanyar amfani da jirgin leken asiri da kuma neman bayanai daga al'umma.

Ya ce jami'an sojojin saman Najeriya ne suka gudanar da binciken a kasashen da ke kusa da Tafkin Chadi wanda suka hada da Chadi, Kamaru, Jamhuriyar Nijar da Najeriya.

Mr Antigha ya yi bayanin cewa wannan ya janyo rugujewar hanyoyin da 'yan ta'addan ke safarar kayayaki da suke kaiwa mayakansu da ke Tumbum Gini, Abadam, Arege, Tumbun rego da Dagaya a tsakanin 7 ga watan Maris zuwa 11 ga watan Maris.

Ya kara da cewa a cikin makonni 4 da suka gabata, an lalata motoccin yaki na Boko Haram guda 70 da kuma wasu kayayakin da suka hada wurin ajiyar man fetur, ma'ajiyar makamai da bindigu.

"Bugu da kari, tun lokacin da aka fara Operation Yancin Tafki, 'yan ta'adda da dama sun mika wuya.

"An karya lagwan mayakan, kuma duk sun harzuka hakan ya janyo suke ta fada tsakaninsu," inji Antigha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel