Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki (Hotuna)

Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja bayan ya kwashe kwanaki shida a mahaifarsa, garin Dauran jahar Katsina, inda ya tafi don yin zaben gwamnoni da yan majalisun da zasu wakilci al’ummar jahar Katsina.

Da tsakar ranar Talata, 12 ga watan Maris ne jirgin shugaba Buhari ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe dake babban birnin tarayya Abuja, tare da uwargidarsa Aisha Buhari, da sauran hadimansa na kusa.

Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki (Hotuna)
Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abubuwa 5 da suka taimaka ma El-Rufai wajen tsallake siradi a Kaduna

Legit.ng ta ruwaito tun a ranar Alhamis data gabata ne Buhari ya wuce garin Daura daga jahar Kaduna bayan ya kaddamar da wata cibiyar tsaro ta sanya idanu da leken asiri da gwamnatin jahar Kaduna ta samar.

Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki (Hotuna)
Fashi barnar aiki: Buhari ya isa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da mulki
Asali: Facebook

A yayin da ya isa Daura kuwa, shugaban kasa Buhari ya samu kyakkyawar tarba daga mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk da yan majalisarsa, inda a washegari, ranar Juma’a, Buhari ya bude sabuwar Masallacin Juma’a daya gina a kauyensu, Dumurkul, a Daura.

Bayan kammala zabe a ranar Asabar, baki sun yi ta zuwa gidan Buhari don tayashi murnar nasarar daya samu a zaben shugaban kasa daya gudana a makonni biyu da suka gabata, daga cikinsu akwai abokansa da suka yi makaranta tare a shekarar 1953.

Sauran sun hada da tawagar Sarkin Daura, gwamna jahar Katsina Aminu Bello Masari tare da kwamishinoninsa da sauran manyan jami’an gwamnatinsa, da kuma yan uwa da abokan arziki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel