An sake kwatawa: gungun mahara sun kashe mutane sun sace shanu a Katsina

An sake kwatawa: gungun mahara sun kashe mutane sun sace shanu a Katsina

Ana fargabar mutuwar mutane da dama bayan wata kazamar hari da wasu gungun yan bindiga marasa Imani da ba’a san ko su wanene ba suka kai a wani kauye dake cikin karamar hukumar Batsari ta jahar Katsina.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun far ma kauyen Bargaja dake cikin karamar hukumar Batsari ne akan babura da dayawa da sanyin safiyar Talata, 12 ga watan Maris, inda suke bude wuta akan jama’an da suka tarar.

KU KARANTA: Abubuwa 5 da suka taimaka ma El-Rufai wajen tsallake siradi a Kaduna

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa ya ga akalla gawarwakin mutane uku zuwa shida bayan tafiyar yan bindigan, haka nan shanu da dama sun bace sama ko kasa, wanda ake zargin maharan ne suka kadasu.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin rundunar Yansandan jahar Katsina game da batun ya ci tura, sakamakon kaakakin rundunar, SP Gambo Isa bai amsa tambayar neman karin bayani da manema labaru suka yi masa game da harin ba.

A wani labarin kuma, wasu yan bindiga sun tare wata mota dake dauke da wani injiniya dan kasar waje a jahar Kano, inda suka yi awon gaba dashi, tare da hallaka direbansa a safiyar yau Talata, 12 ga watan Maris.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 7:40 na safe, ita ma rundunar Yansandan jahar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda Kaakakinta Abdullahi Haruna ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel