Kar ka dauka ka gama samun nasara a kan Atiku - Tanko Yakasai ga Buhari

Kar ka dauka ka gama samun nasara a kan Atiku - Tanko Yakasai ga Buhari

Wani babban jigon Arewa, Tanko Yakasai ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada yayi watsi da dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Yakasai a wata hira da jaridar The Sun yace akwai illa sosai tattare da yasar da Atiku a lissafin mulkin kasar.

Da yake Magana akan shirin Atiku na zuwa kotu akan sakamakonzaben Shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, Yakasari yace Atiku yayi amfani da duk wata dama da yake da ita.

Kar ka dauka ka gama samun nasara a kan Atiku - Tanko Yakasai ga Buhari
Kar ka dauka ka gama samun nasara a kan Atiku - Tanko Yakasai ga Buhari
Asali: UGC

Yace: “A koda yaushe zan goyi bayan mutane da su je kotu saboda kotu ce mai sulhunkarshe. Bana son a cuci kowa. Ya je duk inda yake da dammar baje kwanjinsa.”

Yakasai yace kada Shugaban kasar ya dauka ya gama samun galaba akan Atiku domin a cewarsa shugaba Buhari ya lashe ikon siyasa ne kawai nyayinda Atiku ya lashe ikon tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA KUMA: Na yaga sakamakon zabe ne domin kare dimokradiyya – wakilin dan takarar gwamna a PDP

A wani lamari na daban, mun ji cewa an nemi tsohon babban alkalin alkalai na kasa (CJN), Walter Onnoghen, an rasa shi a gaban kotun ladabtar da ma'aikata ta kasa (CCT), inda ake ci gaba da yin shari'arsa kan zarginsa da gaza bayyana kadarorinsa.

Lauyansa, Adegboyega Awomolo (SAN), a yayin da yake gabatar da dalilin rashin zuwan wanda ya ke karewa, ya shaidawa kotun cewa, a daren ranar Litinin, an sanar da shi cewa mai shari'a Onnoghen na fama da ciwon hakori.

Ya gabatarwa kotun takardar asibiti da ta tabbatar da wannan ikirari na sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel