Kammala Zabe: Al'ummar Kano su kwantar da hankali, su bai wa INEC dama ta gudanar da aikin ta - Sarkin Kano

Kammala Zabe: Al'ummar Kano su kwantar da hankali, su bai wa INEC dama ta gudanar da aikin ta - Sarkin Kano

Biyo bayan rashin tabbatar da sakamakon zabe, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi, ya yi kira ga daukacin al'ummar jihar Kano da su kwantar da hankali tare da zama cikin nutsuwa domin bai wa hukumar zabe damar gudanar da aikin ta.

Yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta kaddamar da cewa zaben wasu jihohin kasar nan bai kammala ba, Sarki Kano ya yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da su kwantar da hankullan su wajen bai wa hukumar INEC damar sauke nauyin da rataya a wuyan ta.

Kammala Zabe: Al'ummar Kano su kwantar da hankali, su bai wa INEC dama ta gudanar da aikin ta - Sarkin Kano
Kammala Zabe: Al'ummar Kano su kwantar da hankali, su bai wa INEC dama ta gudanar da aikin ta - Sarkin Kano
Asali: UGC

Cikin wata hira a farfajiyar fadar sa yayin ganawa da manema labarai, Mai Martaba Sununi ya ce hukumar INEC kadai ke da alhaki a hukumance na sauke nauyin gudanar da zabe tare da bayyana sakamakon sa. Ya yi kira da a bai wa INEC damar gudanar da aikin ta.

A jiya Litinin hukumar INEC ta kaddamar da cewa zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata bai kammala ba sakamakon yadda adadin kuri'u da aka soke ya haura adadin kuri'u na tazara da ke tsakanin manyan 'yan takara biyu masu rinjayen samun nasara.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Cikin zayyana dalilai na soke wasu kuri'u, Farfesa Riskuwa Shehu wanda ya kasance Baturen zabe na jihar kuma shugaban Jami'ar jihar Kebbi ya ce, hakan ya bayu ne sakamakon hargitsi da kuma maimaicin kada kuri'u da suka auku a wasu mazabu cikin kananan hukumomi 22 da ke jihar Kano.

Sarki Sunusi ya yabawa kwazon Kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Muhammad Wakil da kuam sauran hukumomin tsaron dangane da muhimmiyar rawar gani da suka taka wajen tsare rayuka gami da tabbatar da zaman lafiyar al'umma a lokuta na zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel