Na yaga sakamakon zabe ne domin kare dimokradiyya – wakilin dan takarar gwamna a PDP

Na yaga sakamakon zabe ne domin kare dimokradiyya – wakilin dan takarar gwamna a PDP

A yau, Talata, ne rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta gurfanar da Mista Uche Onyeaguocha, wakilin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP tare da wasu mutane uku a gaban wata kotun majistare da ke Owerri bisa zargin su da saba dokokin zabe.

Ragowar da aka gurfanar tare da Onyeaguocha su ne; Steve Asimobi, Paschal Onwukaike da Oliver Enwerenem.

Rundunar ‘yan sanda na tuhumar su da aikata laifuka 10 da ke da alaka da nuna halayen da basu dace ba lokacin zabe, lalata kayan aikin zabe, hana zabe gudana da kuma yaga takardun sakamakon zabe.

Babban majistaren kotun, R.O. Nworka ya amince da bayar da belin ma su laifin kamar yadda lauyan da ke kare su, Mista Loius Alozie (SAN) ya nema. An bayar da belin su ne bisa la’akari da matsayin su.

Na yaga sakamakon zabe ne domin kare dimokradiyya – wakilin dan takarar gwamna a PDP
Cibiyar tattara sakamakon zabe a jihar Imo
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar jami’an tsaro sun kama Onyeaguocha, tsohon mamba a majalisar wakilai, ne a ranar Lahadi bisa zargin sa da yaga sakamakon zaben karamar hukumar Ideato ta Kudu a ofishin hukumar zabe(INEC).

DUBA WANNAN: Akwai abin tarihi guda daya da zan kafa a Najeriya – Buhari

Batn yaga sakamakon zaben da Onyeaguocha ya yi, ya jawo babban baturen zaben gwamna a jihar Imo, Farfesa Franci Atunta na jami’ar noma ta Michael Opara, ya dakatar da sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar.

Da yak e Magana da kamfanin dillancin labarai na kasa, Onyeaguocha ya ce ya yaga sakamakon zaben domin kare dimokraddiya da kuma tsamo jihar Imo daga mulkin mallaka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel