Mahara sun kai farmaki Kano, sun sace wani dan kasar waje tare da kasha direban sa

Mahara sun kai farmaki Kano, sun sace wani dan kasar waje tare da kasha direban sa

- Wasu yan bindiga sun kai farmaki ga wata mota a jihar Kano inda suka sace bakon kasar waje da ke cikin motar

- Sun kuma kashe direban motar bayan sun harbe shi da bindiga

- Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da afkuwar lamarin sannan tace tana kan gudanar da bincike akai

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa a safiyar yau Talata, 12 ga watan Maris ne wasu yan bindiga suka tare wata mota da ke dauke da wani injiniya dan kasar waje.

Bayan haka sai suka yi garkuwa da bakon hauren sannan suka kashe diransa ta hanyar harbinsa da bindiga, jaridar Premium Times ta ruwaito.

An tattaro cewa rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da afkuwar al’amarin.

Wani idon shida ya bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:40 na safiyar yau Talata.

Mahara sun kai farmaki Kano, sun sace wani dan kasar waje tare da kasha direban sa
Mahara sun kai farmaki Kano, sun sace wani dan kasar waje tare da kasha direban sa
Asali: UGC

Wanda aka harbe din dai ya na aiki ne a kan titin kusa da shataletalen Dangi, inda ake aikin titi da gada a Kano, daidai mahadar Titin Gidan Zoo da Zaria Road.

Har zuwa yanzu dai ba a tantance sunan wanda aka sace din ba, kuma ba a san ko dan wace kasa ba ne.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: An nemi Onnoghen a kotun CCT an rasa saboda ciwon hakori

Majiyarmu ta rahoto cewa daga bisani ‘yan sanda sun je sun dauki gawar direban.

Shi kuma Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da afkuwar kisan da yin garkuwar. Ya ce jami’an su na nan sun dukufa bincike.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel