Abubuwa 5 da suka taimaka ma El-Rufai wajen tsallake siradi a Kaduna

Abubuwa 5 da suka taimaka ma El-Rufai wajen tsallake siradi a Kaduna

Sanannen abu ne gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya sake lashe zaben gwamnan jahar Kaduna karo na biyu bayan ya samu kuri’u 1,045,417, inda abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Isah Aashiru ya samu 814,244, bambamcin kuri’u 231,173.

Sai dai kafin wannan zabe, farfajiyar siyasar jahar Kaduna ta cika da rashin tabbas, inda masana siyasar jahar keta hasashe daban daban game da yiwuwar Malamin gwamnan ya samu nasara a zaben, ba don komai ba sai don ya dauko Mace, kuma Musulma a matsayin mataimakiyarsa.

KU KARANTA: Al’ummar garin Zaria sun bayyana farin cikin samun nasarar El-Rufai

Don haka Legit.ng ta kawo muku wasu daga cikin abubuwan da suka hadu, suka baiwa El-Rufai nasara a wannan zabe, kamar yadda duk wani mai bin diddigin siyasan jahar Kaduna zai iya hakaitowa.

Daukan mataimakiya Musulma Mace

El-rufai ne zababben gwamnan jahar Kaduna na farko daya fara dauko Mace, Hajiya Hadiza Balaraba a matsayin mataimakiyarsa, kuma ya daukota daga kudancin Kaduna, yankin da suka saba bada dan takarar gwamnan, amma Kirista, saboda Kiristoci ne mafiya rinjaye a yankin.

A iya cewa gwamnan ya zunguro sama da kara, tun bayan da Kiristoci da kabilun kudancin Kaduna suka nuna basa tare da dashi saboda wannan mataki, amma ko gezau, ba karaya ba, ya dinga fadin dacewar Hadiza na rike wannan mukami a matsayinta na kwararriyar likita.

Amma wannan mataki yayi ma Musulman Kaduna dadi, inda suke ganin anyi tuwona maina kenan, don haka suka mara ma El-Rufai baya, a haka har ya kai labari.

Ayyukansa

Babu wani mazaunin jahar Kaduna da zai yi ikirarin El-Rufai baya aiki, sai dai wasu suna ganin aikin bai kai yadda ake zuzuta gwamnan zai yi farkon mulkinsa ba, idan ka duba daga daukan Malamai 25,000, daukan ma’aikatan KASTELEA 2,250, daukan malaman asibiti fiye da 1000 da gyaran kananan asibitioci 255.

Sauran sun hada da gyaran tituna da gina sababbi, gyara da gina sababbin makarantu, ciyar da daliban Firamari, kawo sauye sauye a aikin gwamnati, daukan ma’aikatan hukumar tattara haraji, taimaka ma matasa da tallafin fara sana’a na KADSTEP, da ireiren aikacen sun taimaka gaya wajen bashi kuri’un da yake bukata.

Siyasar addini da kabilanci

Jahar Kaduna ta dade tana samun rikice rikicen addini da kabilanci, don haka ba’a raba siyasar jahar da bambance bambancen addini ko na kabilanci, musamman idan har zabe ta kunno kai. Ko a wannan zaben ma an samu irin haka, inda aka jiyo Fastoci suna goyon bayan Isa Ashiru saboda ya dauki Kirista a matsayin mataimaki, yayin da Malaman Musulunci suka goyi bayan El-Rufai saboda Hadiza Balarabe.

Haka nan matsalar tsaro dake faruwa a kudancin Kaduna ta kara dagula siyasar jahar,inda kiristocin yankin suka nuna rashin jin dadinsu yadda gwamna ke tafiyar da tsaron yankin, yayin da Musulman dake yankin suka yi na’am da kamun ludayinsa.

Wannan matsala tasa hatta jama’an wasu jahohin na son ganin yadda zata kaya a Kaduna, inda yawancin Kiristocin ciki da wajen Kaduna ke nuna rashin amincewa da gwamnan, Musulmai daga ciki da wajen jahar kuma suka rungumeshi, wannan rabuwan kan ma ya raba kuri’un jahar tsakanin APC da PDP.

Siyasar Buhari

Daga cikin jahohin da farin jinin shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi tasiri akwai jahar Kaduna, musamman duba da kyakkyawar alakar dake tsakanin Buhari da gwamnan, kuma Buhari yayi nuni da magoya bayansa dasu zabi El-Rufai, don haka babu ko tantama hakan yayi tasiri a nasarar gwamnan.

Karfin iko

Kasancewarsa gwamna, El-Rufai ya bayyana cewa ba zai zura idanu wasu yan tsiraru su tayar da hankali a yayin zaben 2019 ba, don haka an girke jami’an tsaro a duk inda aka san za’a iya samun tashin tashina, wanda hakan yasa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, da ba don haka ba wasu ka iya tayar da hankali, wanda hakan zai janyo kashe zabe a wurare da dama.

Sai dai duk da wannan nasara ta El-Rufai, Isa Ashiru ya dauki alwashin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun sauraron koke koken zaben gwamna domin ta kwatan masa hakkinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel