Da duminsa: An nemi Onnoghen a kotun CCT an rasa saboda ciwon hakori

Da duminsa: An nemi Onnoghen a kotun CCT an rasa saboda ciwon hakori

- Rahotanni sun bayyana cewa an nemi Walter Onnoghen, an rasa shi a gaban kotun CCT inda ake ci gaba da yin shari'arsa kan zarginsa da gaza bayyana kadarorinsa

- Lauyansa, Adegboyega Awomolo (SAN), ya shaidawa kotun cewa, mai shari'a Onnoghen na fama da ciwon hakori da kuma hawan jini

- Da wannan kotun ta dage sauraran karar har sai ranar Litinin, 18 ga watan Maris, bayan da lauyan mai kara ya tabbatar da rashin lafiyar Onnoghen

Rahotanni sun bayyana cewa an nemi tsohon babban alkalin alkalai na kasa (CJN), Walter Onnoghen, an rasa shi a gaban kotun ladabtar da ma'aikata ta kasa (CCT), inda ake ci gaba da yin shari'arsa kan zarginsa da gaza bayyana kadarorinsa.

Lauyansa, Adegboyega Awomolo (SAN), a yayin da yake gabatar da dalilin rashin zuwan wanda ya ke karewa, ya shaidawa kotun cewa, a daren ranar Litinin, an sanar da shi cewa mai shari'a Onnoghen na fama da ciwon hakori.

Ya gabatarwa kotun takardar asibiti da ta tabbatar da wannan ikirari na sa.

KARANTA WANNAN: Zaben Gombe: Nafada ya taya Yahaya murnar lashe zabe, ya ce ba zai je kotu ba

Da duminsa: An nemi Onnoghen a kotun CCT an rasa saboda ciwon hakori
Da duminsa: An nemi Onnoghen a kotun CCT an rasa saboda ciwon hakori
Asali: Depositphotos

Lauyan bangaren da ke kara, Aliyu Umar (SAN) ya tabbatar da cewa ya samu kwafi na takardar rashin lafiyar wanda ake karar, dauke da sa hannun Dr. Francis Uche, daraktan sashen lafiya na asibitin Ideal Medical Services.

Ya ce duk wani bincike da za ayi ba zai tasiri ba la'akari da bayanin likitan na cewa jinin wanda ake tuhumar ya haura zuwa 410/121, yana mai cewa, "a matsayinsa na dattijo, na san hatsarin da ke tattare da hawan jinin na sa."

Da wannan, shugaban kotun, Danladi Umar, ya yanke hukuncin cewa, an dage zaman shari'ar har sai ranar Litinin bisa la'akari da rashin lafiyar wanda ake tuhumar, inda a karshe aka cimma matsaya kan ci gaba da sauraron karar a ranar 18 ga watan Maris.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel