Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bar Daura zuwa Abuja

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bar Daura zuwa Abuja

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Uwargidarsa, Hajiya Aisha a ranar Talata, 12 ga watan Maris sun bar Daura zuwa Abuja

- Buhari da iyalansa da wasu hadimansa sun je Daura ne domin kada kuri'arsu na zaben gwamna da na yan majalisar jiha

- Shugaban kasar ya samu rakiyan sarkin Daura da wasu yan uwansa zuwa wajen shiga jirgi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Uwargidarsa, Hajiya Aisha a ranar Talata, 12 ga watan Maris sun bar Daura inda za su koma Abuja bayan kada kuri’a a zabbukan gwamna da majalisan jiha wanda aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bar Daura zuwa Abuja
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya bar Daura zuwa Abuja
Asali: Twitter

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa shugaban kasar ya bar Daura a ranar Talata da misalin karfe 11:10 na safe a jirgin shugaban kasa mai lamba NAF-541 tare da hadiman sa da yan uwansa.

Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk tare da yan uwan shugaban kasan sun yi masa rakiya zuwa wajen shiga jirgi.

KU KARANTA KUMA: Direban jirgi yayi durowar gaggawa bayan Fasinja ta manta da jaririn ta

NAN ta rahoto cewa Buhari ya kasance a Daura tun a ranar Alhamis don kada kuri’arsa a zaben gwamna da majalisan jiha wanda aka gudanar a ranar Asabar da ya gabata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel