Bidiyon yadda Gwamna Bello ya yi murnar lashe zabe cikin sabon salo mai kayatarwa

Bidiyon yadda Gwamna Bello ya yi murnar lashe zabe cikin sabon salo mai kayatarwa

Bayan kammala zaben gwamnonin jihohi da akayi a ranar Asabar da ta gabata, gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya yi bayyana farin cikin sa a kan nasarar da ya samu cikin wani sabon salo da ya nuna a shafin sada zumunta.

Gwamnan na jam'iyyar All Progresive Party APC ya haska bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya ke murnar lashe zaben.

A cikin bidiyon, an haska gwamnan yana motsa jiki a kan na'urar gudu. Sai dai ba gudun kadai ya ke yi ba, ana iya gani yana murna yana daga hanayensa biyu da yatsu hudu da ke nuna alamar tazarce wato 4 + 4 wanda alama ce ta taken Next Level na jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja

Ya kuma rika taka rawa a yayin da ya ke sauraran waka a kunnensa yana kallon na'uarar daukan bidiyon.

An yiwa bidiyon lakabi da "Lets go there!!! Congratulations APC Congratulations NIGERIA. GYB 2019 is a goal".

A wani labarin, anyi sace wasu ma'aikatan hukumar INEC shida a garin Lokoja yayin zaben 'yan majalisun jiha a ranar Asabar amma daga baya an sako su.

Sace ma'aikatan zaben yana daya daga cikin matsalolin da aka fuskanta yayin gudanar da zaben da aka samu tashe-tashen hankula da yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel