Mun amince da hukuncin INEC da kyakyawar zuciya – Dan takarar gwamnan APC a Sokoto

Mun amince da hukuncin INEC da kyakyawar zuciya – Dan takarar gwamnan APC a Sokoto

Dan takaran gwamna a jam’iyyan All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto a ranar Litinin, 11 ga Maris ya ce ya amince da hukuncin da INEC ta yaanke akan sakamakon zaben gwamna a jihar bayan ta bayyana zaben a matsayin ba kammalalle ba.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Gawon Nama, Sokoto, gidan shugaban Sanatocin Arewa kuma jagoran kamfen din Shugaban kasa a yankin arewa maso yamma, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, dan takaran gwamnan a jihar yace, “ jam’iyyar APC, shuwagabanninta da magoya bayanta sun kasance masu bin doka, saboda haka, mun amince da shawarar da hukumar INEC ta yanke."

Mun amince da hukuncin INEC da kyakyawar zuciya – Dan takarar gwamnan APC a Sokoto
Mun amince da hukuncin INEC da kyakyawar zuciya – Dan takarar gwamnan APC a Sokoto
Asali: UGC

Matashi dan takaran gwamnan ya cigaba da korafi akan yanda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta keta doka a lokacin da ake gudanar da zabe, kamar siyan kuri,u, yin amfani da jami’an tsaron bogi, razana masu kada kuri’a, da makamancin haka.

KU KARANTA KUMA: Direban jirgi yayi durowar gaggawa bayan Fasinja ta manta da jaririn ta

A cewar Aliyu Sokoto, yana mai jinjina ma masu zabe, magoya bayan APC a jihar akan yunkuri da suka yi na fitowa kwansu da kwarkwatansu a ranar 9 ga watan Maris, 2019, inda suka zabi yan takaran APC a gwamna da majalisan jiha.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel