Babagana Zulum: Wanda ya rika tuka motar kabu-kabu a 1984 zai mulki Borno

Babagana Zulum: Wanda ya rika tuka motar kabu-kabu a 1984 zai mulki Borno

Ku na da labari cewa Babagana Umara Zulum, shi ne ya lashe zaben jihar Borno da aka yi a karkashin jam’iyyar APC. Gana Umara Zulum yayi aikin kabu-kabu na shekaru 15 a lokacin da a rayuwar sa.

Kafin Babagana Umara Zulum yayi takara, ya taba hira da ‘yan jarida inda ya bada labarin yadda ya rika wahala lokacin yana karamin yaro domin ganin yayi karatu. Wannan ta sa ya rika takawa a kafa yana noma a gonar Mahaifin sa.

Umara Zulum yace kullum sai ya taka kafa-ya-kafa na tsawon tafiyar kilomita 7 a cikin kauyen Loskuri da ke cikin karamar hukumar Mafa a jihar Borno. Bayan ya girma kuma yace ya zama Direban motar haya duk don neman halal.

KU KARANTA: Mutanen Yankin Gabas sun yi Gwamna Farfesa a zaben 2019

Babagana Zulum: Wanda ya rika tuka motar kabu-kabu a 1984 zai mulki Borno
Zulum ya zama Gwamna bayan yayi aikin Direba a da
Asali: Twitter

Farfesan yace yayi aikin kabu-kabu ne na tsawon shekaru 16; tsakanin 1984 zuwa cikin shekarar 1999. Zulum yace a wancan lokaci ya tuka motocin haya iri-iri musamman Peugeot 404, da kuma doguwar motar haya kirar bas a cikin Borno.

A wasu lokutan ma dai wannan Bawan Allah yace ya rika tuka gingimari da sauran manyan motoci masu daukar kayan itace a daji. Umaru Zulum yake bada labarin cewa a haka ne ya koyi gyaren motoci iri-iri saboda da yayi da aiki da su.

A wasu lokutan ma dai Zulum yace sai da ya koma aikin markade, inda ya samu na’urar da yake yi wa jama’a surfe a gida duk domin ya samu halin zuwa makaranta a lokacin yana yaro. A watan jibi ne za a rantsar da shi a matsayin Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel