Direban jirgi yayi durowar gaggawa bayan Fasinja ta manta da jaririn ta

Direban jirgi yayi durowar gaggawa bayan Fasinja ta manta da jaririn ta

A wani lamari na gaggawa wanda ba kasafai yake aukuwa ba, jiragen sama kan koma filin jirgi domin karban wasu kayayyaki da aka manta.

Wani lamari na gaggawa mai cike da al’ajabi ya afku a filin jirgin saman Saudiyya ba Sarki Abdulaziz bayan wata mata ta manta da jaririnta sabuwar haihuwa a filin jirgin saman.

A bisa ga labaran Gulf, duk da tsananin shakuwar da ke tsakanin uwa da danta, wannan mata da ba’a bayyanata ba ta shige jirgin kasar Saudiyya ba tare da wata damuwa ba.

Ta hankalta cewar ta baro jaririn nata ne a dakin jiran matafiya bayan jirginsu ya tashi daga filin jirgin.

Direban jirgi yayi durowar gaggawa bayan Fasinja ta manta da jaririn ta
Direban jirgi yayi durowar gaggawa bayan Fasinja ta manta da jaririn ta
Asali: UGC

A take bayan ta lura da shirmen da ta tafka, sai ta sanar da ma’aikatan jirgin cewa ta manta da jaririnta a filin jirgi inda hakan ya turasasa matukin jirgin mai lamba SV832 daga babbar birnin Saudiyya, Jeddah juyawa zuwa Kuala Lumpur.

Lamarin ya ba dukkanin ma’aikatan jirgin harda fasinjoji mamaki matuka.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Ya zama dole ku kare hakki da ra’ayin yan kasa – Shugaban Alkalan Najeriya ga Alkalai

Bidiyon lokacin da matukin jirgin ke bayar da sanarwar komawarsa filin jirgin ya yi fice a kafofin sada zumunta inda mutane ke ta mamakin yadda za a yi ace mutun ya iya mantawa da dansa a wani wuri.

Daga bisani dai matar ta sake haduwa da jaririn nata.

Allah ya kyauta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel