Zabe: Ya zama dole ku kare hakki da ra’ayin yan kasa – Shugaban Alkalan Najeriya ga Alkalai

Zabe: Ya zama dole ku kare hakki da ra’ayin yan kasa – Shugaban Alkalan Najeriya ga Alkalai

- Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammad ya yi jan kunne gaa alkalan kasar yayinda ake shirin fara sauraron korafe-korafe akan zaben 2019

- Mulhammad ya jadadda cewa ya zama dole Alkalan da kare hakki da ra'ayin jamaá

- A cewarsa ta hakan ne kadai za a ji gajiyar dorewar damokradiyya a kasar

Gababannin fara fafatawa kan forafe-korafen da ake zatton za su karu daga zaben kasar da ya gudana na wannan shekakaran, shugaban alkalan Najeriya (CJN), justis Tanko Muhammad a jiya ya bukacki alkalai a fadin kasar da su kare hakkin al’umma.

Muhammad yayi gargadin cewa damokardiyya za ta inganta ne a kasar idan aka kare yancin al’umma ta hanyar nuna tarayya a zabe mai tattare da gaskiya.

Zabe: Ya zama dole ku kare hakki da ra’ayin yan kasa – Shugaban Alkalan Najeriya ga Alkalai
Zabe: Ya zama dole ku kare hakki da ra’ayin yan kasa – Shugaban Alkalan Najeriya ga Alkalai
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa bangaren shari’a ce kadai yankin gwamnati wacce kundin tsari ya bai wa karfin sasanta tsakanin “masu karfi” da “marasa karfi”.

Shugaban alkalan yayi jawabi ne a yayin bude taron bikin refresher course na 2019 na alkalai a Babbar Cibiyar kungiyar Alkalai, a Abuja.

KU KARANTA KUMA: PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamna a Borno

Yayinda take gabatar da jawabi, mai gudanarwa a cibiyar NJI, Justis R.PI Bozimo, ta ce taken Refresher Course na wannan shekaran shine: Repositioning the Judiciary for Better Justice Delivery”, ya dace idan aka yi la’akari da cewa martabar kotu da dokoki sun kasance tsarin addalci kuma tushen damokardiyya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel