Zaben 2019: INEC ba ta tabuka komai ba, dole Yakubu ya yi murabus - Onitiri

Zaben 2019: INEC ba ta tabuka komai ba, dole Yakubu ya yi murabus - Onitiri

- Chief Sunbo Onitiri, ya yi Allah-wadai da hukumar INEC kan yadda ta nuna bangaranci a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da ta gudanar

- Onitiri ya yi kira ga Farfesa Mahmood Yakubu da ya taimaka cikin ruwan sanyi ya yi murabus daga wannan mukami na sa da kuma baiwa 'yan Nigria hakuri

- Ya yi kira ga 'yan Nigeria da su sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sake gudanar da sake fasalin tsarin demokaradiyyar kasar

Dan takarar mazabar Legas ta Tsakiya a majalisar dattijai ta kasa karkashin jam'iyyar PDP, Chief Sunbo Onitiri, ya yi Allah-wadai da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC kan yadda ta nuna bangaranci a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da ta gudanar a fadin kasar.

Ya kuma yi kira ga shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ya taimaka cikin ruwan sanyi ya yi murabus daga wannan mukami na sa da kuma baiwa 'yan Nigria hakuri kan gudanar da "mummunan zabe, mai cike da magudi da nuna bangaranci, wanda ba a ta samun zabe mai muni a tarihin zaben Nigeria irinsa ba."

A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Legas a ranar Litinin, ya ce: "Yanayin yadda INEC ta gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ya harzuka jama'a suka kauracewa zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki.

KARANTA WANNAN: Ta bayyana: Yadda rundunar sojin sama ta ragargaza mabuyar 'yan ta'adda a Borno

Zaben 2019: INEC ba ta tabuka komai ba, dole Yakubu ya yi murabus - Onitiri
Zaben 2019: INEC ba ta tabuka komai ba, dole Yakubu ya yi murabus - Onitiri
Asali: UGC

"Wannan ya nuna zanga zanga cikin lumana ba tare da gangami ba da 'yan Nigeria suka yi biyo bayan cire tsammani daga hukumar INEC. Gazawar fitowar jama'a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki ya nuna cewa INEC ta gurguntar da tsarin demokaradiyyar Nigeria."

Ya yi kira ga 'yan Nigeria da su sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sake gudanar da sake fasalin tsarin demokaradiyyar kasar.

Ya ce: "Ina mai yin Allah-wadai da yadda aka rinka cafke mambobin jam'iyyar adawa, inda mambobin jam'iyya mai mulki suka ci gaba da karya dokokin zaben kasar, da sanin cewa za su samu kariya.

"Duba da zaben shuaban kasa da na wamnoni, INEC ta yi nasarar banzatar da dumbin dukiyar kasaar, tare da lalata tsarin demokaradiyya da kuma cin mutuncin dukkanin tunanin 'yan Nigeria. Hakika INEC ta rasa dukkanin wani mutuncinta a idon jama'a,"

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel