Zabe: Rundunar yan sandan Kano ta yi gargadi akan rushewar zaman lafiya

Zabe: Rundunar yan sandan Kano ta yi gargadi akan rushewar zaman lafiya

Rundunar yan sandan jihar Kano ta gargadi mazauna jihar akan ayyukan da ka iya rusa zaman lafiyar da ke warzuwa a jihar tun bayan kaddamar da rashin kammala zaben gwamna a jihar.

Kakakin rundunar yan sandan, DSP Abdullahi Haruna ya bayar da gargadin a wani jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 11 ga watan Maris a Kano.

Ya kara da cewa akwai bukatar mutanen jihar su ci gaba da kwantar da hankalinsu sannan su guje ma duk wani abu da ka iya haifar da barkewar rikici da kuma karya doka da oda.

Kakakin yan sandan yayi gargadin cewa rundunar ba za ta nade hannu sannan ta bari wasu yan jagaliya su zo su tarwatsa zaman lafiyar da ake ciki ba akan sakamakon zabe.

Zabe: Rundunar yan sandan Kano ta yi gargadi akan rushewar zaman lafiya
Zabe: Rundunar yan sandan Kano ta yi gargadi akan rushewar zaman lafiya
Asali: Facebook

A cewarsa, duk wanda aka kama yana karya doka ko kuma yana kokarin tayar da fitina za a kama shi sannan a mika shi kotu.

KU KARANTA KUMA: PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamna a Borno

“Rundunar yan sandan jihar na son yin gargadi ga mazauna jihar, musamman matasa, das u janye daga ayyukan da ka iya haddasa rikici a tsakanin mutanen jihar.

“Hukumar yan sandan jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka kama yana kokarin haddasa fitina,” Inji Haruna.

Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana kaddamar da zaben gwamna da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris a matsayin ba kammalalle ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel